en
stringlengths
4
1.32k
ha
stringlengths
4
1.4k
Medical and nursing education, including providing trainees with simulated patient encounters, and;
Ilimin likitanci da malaman jinya, wanda ya haɗa da samar da masu bada horo da suke da sani game da marasa lafiya, da kuma;
Neurological conditions are the leading cause of disability adjusted life years (DALYs) and account for about 9 million deaths per year.
Yanayin ƙwaƙwalwa su ne kan gaba wajen haddasa samar da nakasa a shekarun rayuwa kuma mutane miliyan 9 na mutuwa a duk shekara.
Not only were there more outbreaks, but the outbreaks were larger.
Ba wai kawai an sami ƙarin ɓarkewar cutar ba, amma annobar ta ƙara girma.
Compared to previous rounds of national climate plans, health-inclusive and health-promoting climate targets and policies are increasingly being developed for mitigation, adaptation, means of implementation, Loss and Damage, and long-term sustainable development strategies.
Idan aka kwatanta da zagayen da suka gabata na tsare-tsare na yanayi na ƙasa, ana ci gaba da samar da manufofin yanayi da manufofin da suka haɗa da lafiya da inganta lafiya don ragewa, daidaitawa, hanyoyin aiwatarwa, Asara da ɓarna, da dabarun ci gaba mai ɗorewa na dogon lokaci.
These strategies include reducing risk factors, developing standards of care, enhancing health system capacity to care for patients with CVD, and monitoring disease patterns and trends to inform national and global actions.
Waɗannan dabaru sun haɗa da rage abubuwan da suke haifarwa da samar da tsare-tsaren ba da kulawa da da bunƙasa ingancin tsarin lafiya domin kulawa da marasa lafiya da suke fama da ciwon zuciya da jijiyoyin jini, da kuma kulawa da sakon sababbin cututtuka domin ɗaukar mataki a ƙasa da duniya.
They can also range from small releases to full-scale major emergencies.
Za su iya kuma dinga fita daga kaɗan-kaɗan zuwa fita sosai har a buƙaci taimakon gaggawa.
Response: To improve health equity, evidence-informed action is needed:
Amsa: Domin inganta daidaito a harkar lafiya, akwai buƙatar ɗaukar mataki ta hanyar shaidu.
WHO organizes these consultations with an advisory group of experts gathered from WHO Collaborating Centres and WHO Essential Regulatory Laboratories to analyse influenza virus surveillance data generated by the WHO Global Influenza Surveillance and Response System (GISRS).
WHO ta shirya waɗannan shawarwari tare da gungun ƙwararrun masu bada shawara da suka taru daga Cibiyoyin Haɗin gwiwar WHO da ɗakunan gwaje-gwaje masu mahimmanci na WHO don nazarin bayanan sa ido kan cutar mura da WHO Global Influenza Surveillance and Response System (GISRS) ta samar.
This is recommended in areas where large numbers of people are infected.
Ana bada shawarar amfani da wannan hanyar inda mutane da yawa suka kamu da cutar.
Released in the lead up to the upcoming United Nations Framework Convention on Climate (COP-28), this comprehensive Framework is designed to enhance the resilience of health systems while simultaneously reducing greenhouse gas emissions to help safeguard the health of communities worldwide.
An fitar da shi a kan gaba har zuwa taron Tsarin Mulki na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yanayi (COP-28), wannan cikakken Tsarin an tsara shi don haɓaka juriyar tsarin kiwon lafiya tare da rage hayaƙi mai gurɓata yanayi don taimakawa kare lafiyar al'ummomin duniya.
Symptoms: Guinea-worm disease is rarely fatal.
Alamomi: cutar kurkunu (Guinea-worm) ba kasafai ta cika zama me kisa ba.
WHO Response: WHO is continuously updating guidance on the clinical use of oxygen for different diseases and health conditions.
Martanin WHO: WHO tana ci gaba da sabunta jagora kan amfani da iskar oxygen na asibiti don cututtuka daban-daban da yanayin lafiya.
Although neutralizing antibody titres have been shown to be important correlates of protection from SARS-CoV-2 infection and of estimates of vaccine effectiveness, there are multiple components of immune protection elicited by infection and/or vaccination.
Ko da yake an nuna neutralizing antibody titres a matsayin muhimmin ma'auni na kariya daga kamuwa da cuta ta SARS-CoV-2 da kuma kimanta tasirin rigakafin, akwai abubuwa da yawa na kariya ta rigakafi da ke haifar da kamuwa da cuta da/ko rigakafin.
The funding would go to the African Region, with US$ 334 million; the Eastern Mediterranean Region, with US$ 705 million; the European region, with US$ 183 million; the Western Pacific Region, with US$ 15.2 million; the South-East Asia Region, with US$ 49 million; and the Americas Region, with US$ 131 million.
Tallafin yana isa ga Yankin Afrika, tare da US$ miliyan 334; Yankin Eastern Mediterranean, da US$ miliyan 705; Yankin Turai, da US$ miliyan 183; Yankin Western Pacific, da US$ miliyan 15.2; Yankin South East Asia, da US$ miliyan 49; da Yankin Amurka, da US$ miliyan 131.
Hospital directors and health workers are now facing an agonizing choice: abandon critically ill patients amid a bombing campaign, put their own lives at risk while remaining on site to treat patients, or endanger their patients’ lives while attempting to transport them to facilities that have no capacity to receive them.
Daraktocin asibiti da ma'aikata lafiya na fuskantar zaɓin dole : banzatar da majinyatan da ke tsaka mai wuya a tsaka da fashewar boma-bomai , sun sanya rayukan su cikin hatsari a yayin da suke cigaba da kasancewa a waɗannan wajaje don kula da majinyata ko kuma su sanya majinyatan su cikin hatsari a yayin da su ke ƙoƙarin jigilar su zuwa asicitocin ba ba su da ƙarfin karɓan su.
This includes norms, behaviours and roles associated with being a woman, man, girl or boy, as well as relationships with each other.
Hakan ya haɗa da al'adu da ɗabi'u da kuma matakai da suke da alaƙa da kansancewa mace ko babban mutum ko yarinya ko kuma yaro, da kuma dangantakar da ke tsakanin junansu.
Prevention: In 2020, 22% of children under age 5 worldwide (149.2 million) suffered from stunting, a decline from 24.4% in 2015.
Kariya: a shekarar 2020, kaso 22% na yaran da suke ƙasa da shekaru 5 a faɗin duniya (wato yara miliyan 149.2) sun yi fama da tsakurewar girma wato ragi daga kaso 24.4% a shekarar 2015.
facilitating the identification and acquisition of necessary materials (such as personal protective equipment) appropriate to the event;
Samar da kuma kula da kayan aiki ( kamar kayan bada kariya ga mutane ) wanda ya dace da yanayin;
Hot ashes can also start wildfires.
Sannan ɓurɓushin duwatsu na iya tayar da wutar daji.
Reasons for this include:
Dalilan hakan ya haɗa da:
With so much civilian infrastructure in Gaza damaged or destroyed in nearly two weeks of constant bombings, including shelters, health facilities, water, sanitation, and electrical systems, time is running out before mortality rates could skyrocket due to disease outbreaks and lack of health-care capacity.
Yayin da aka yi rushe-rushen gine-ginen fararen hula a Gaza a cikin kusan sati biyu na hare-haren boma-bomai, waɗanda suka haɗa da gidaje da asibitoci da ruwa da wuraren kula da tsabtar muhalli da kuma wutar lantarki, lokaci na ƙara ƙurewa kafin adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar annoba ya ƙaru da kuma rashin samun isassun kayan kula da majinyata a asibiti.
“I welcome this commitment by world leaders to provide the political support and direction needed so that WHO, governments and all involved can protect people’s health and take concrete steps towards investing in local capacities, ensuring equity and supporting the global emergency health architecture that the world needs.”
Ina maraba da wannan alƙawarin da shugabannin duniya suka yi na ba da goyon baya na siyasa da alƙiblar da ake buƙata ta yadda WHO, gwamnatoci da duk waɗanda abin ya shafa za su iya kare lafiyar mutane, tare da ɗaukar ƙwararan matakai don saka hannun jari a cikin ayyukan gida, tabbatar da daidaito da tallafawa gine-ginen kiwon lafiya na gaggawa na duniya wanda duniya ke buƙata. .”
Lack of social connection carries an equivalent, or even greater, risk of early death as other better-known risk factors – such as smoking, excessive drinking, physical inactivity, obesity, and air pollution.
Rashin dangantakar zamantakewa na ɗaukar daidaito ko kuma mafi yawan haɗarin mutuwa da wuri ko abin da aka fi sani da abu mai haɗari - kamar su shan taba da shan giya da yawa da rashin motsa jiki da ƙiba da gurɓatacciyar iska.
After the presentations, Committee Members and Advisors proceeded to engage the Secretariat and the presenting countries in a question-and-answer session.
Bayan kammala jawaban ne sai aka shiga sashin tambaya-da-amsasoshi ga ƙasashen da suka gabatar da jawaban.
Other serious consequences of foodborne diseases include kidney and liver failure, brain and neural disorders, reactive arthritis, cancer, and death.
Wasu daga cikin munanan sakamakon cututtukan abinci sun haɗa matsalolin ƙoda da hanta da ƙwaƙwalwa da matsalolin jijiya da ciwon gaɓoɓi da ciwon daji da kuma asarar rai.
Delegates support maintaining momentum and innovations to end TB
Wakilai suna goyan bayan ci gaba don ƙoƙarin smar da sabbin abubuwa don kawo ƙarshen tarin fuka
Overview: Radiation emergencies are non-routine situations or events that require a prompt action to mitigate a radio-nuclear hazard or its adverse consequences for human life, health, property or the environment.
Taƙaitawa: Yanaye-yanayen da tartsatsin haske kan iya cutarwa lokuta ne da ba kasafai ake samun su ba da suke buƙatar matakin gaggawa domin rage illar haske na nukiliya a kan rayuwar ɗan'adam da lafiya da dukiya ko kuma muhalli.
Global health ethics
ƙa'idojin lafiya na duniya
1. Early diagnosis identifies symptomatic cancer cases at the earliest possible stage.
1. Saurin yin gwaji yana sa a gano alamomin daji a farkon mataki na farko .
Up to 90% of those infected experience no or mild symptoms and the disease usually goes unrecognized.
Har zuwa kashi casa'in 90 cikin ɗari 100 na waɗanda suka kamu da cutar babu ko ƙananan alamun cutar kuma yawanci ba a gane cutar ba.
The Committee felt it was still too early to discontinue the PHEIC as the risk of exportation of both WPV and cVDPVs remains significant and the removal of the PHEIC may send the wrong message at this critical juncture in polio eradication.
Kwamitin yana ganin cewa yayi wuri a daina yin PHEIC saboda har yanzu akwai haɗarin shigowa da WPV da CVDPV sannan cire PHEIC zai iya tura sako ba daidai ba a wannan gabar mai haɗari ta kawar da cutar polio.
The EDL provides guidance based on the latest evidence, to countries for creating or updating their national lists of essential IVDs.
Jerin na samar da ilimi gwargwadon sababbin shaidu, ga ƙasashe don ƙirƙirowa ko sabunta jarinsu na ƙasa na abubuwan da ake buƙata a gwaje-gwajen gano cuta a wajen jikin mutum.
WHO collaborates with UN partners to disseminate global guidance on the assessment of micronutrient status and effective micronutrient interventions.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta haxa hannu da Majalisar Dinkin Duniya don yaxa manufar ta a duniya, bisa qarancin abinci mai gina jiki da ingantattun hanyoyin samar da abincin.
Furthermore, the WHO Global COVID-19 Vaccination Strategy, published in July 2022, also calls for vaccines with improved durability and breadth of protection.
Bugu da ƙari, Tsarin Allurar rigakafin COVID-19 na Duniya na hukumar lafiya ta duniya wato WHO, wanda aka wallafa a watan Yulin 2022, ya kuma yi kira ga alluran rigakafi tare da inganci wajen dorewa da yawan ba da kariya.
It remains an important cause of death among young children globally, despite the availability of a safe and effective vaccine.
Ya kasance muhimmin sanadin mace-mace tsakanin yara ƙanana a duniya, duk da samun rigakafi mai inganci.
This can save thousands of lives every year.”
Wannan zai iya ceton dubban rayuka a kowace shekara."
applying insect repellent to skin or clothing that contains DEET, IR3535 or icaridin according to the product label instructions.
Shafa maganin sauro a jiki ko sanya kaya da suke ɗauke da DEET, IR3535 ko icaridin kamar yadda sunan kayan ya bayyana.
Quality health services should be: effective; safe; people-centred; timely; equitable; integrated; and efficient.
Ingantattun ayyukan kiwon lafiya yakamata su kasance: masu tasiri; aminci; nanu kulaw; akan lokaci; masu adalci; haɗaɗɗe; da inganci.
She has served as Advisor to the Director-General of WHO on Mental Health and Autism.
Ta riƙe mukamin mai ba da shawara ga Babban Daraktan WHO a kan lafiyar ƙwaƙwalwa da Autism.
Intensify efforts to ensure vaccination of mobile and cross­-border populations, Internally Displaced Persons, refugees and other vulnerable groups.
Tabbatar da an samar da rigakafi ga fatake da matafiya, 'yan gudun hijira, mutanen da yaƙi ya raba su da muhallansu, da sauransu.
The risk of death is 3 times higher in low-income than high-income countries, yet low-income countries have just 1% of the world’s motor vehicles.
Haɗarin mutuwa ya ninka sau uku a ƙasashe masu ƙaramin karfi fiye da masu tasowa, duk da haka ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi suna da kashi 1% na motocin duniya.
Environmental risks have an impact on the health and development of children, from conception through childhood and adolescence and also into adulthood.
Hatsarorrin muhalli suna da tasiri a kan lafiya da girman yara, daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa yarinta da lokacin tasawa da kuma lokacin balaga.
It increases risky health behaviours (e.g., eating an unhealthy diet, smoking).
Tana ƙara haɗarin halayyar lafiya (misali, cin abinci mara kyau da shan taba).
There are three recommended typhoid vaccines:
Akwai alluran rigakafin taifot uku da aka ba da shawara:
Today, on the International Day of Zero Tolerance for Female Genital Mutilation, we reaffirm our dedication to the girls and women who have been subjected to this grave violation of human rights.
A yau, a Ranar Ƙin Amincewa da Kaciyar Mata ta Duniya, muna tabbatar da goyon bayanmu ga yara da manya mata waɗannan suka haɗu da wannan keta haƙƙin ɗan’adam.
A consistent supply of blood is a cornerstone of any health-care system, but this relies on regular donations and effective health-care infrastructure.
Yawan bayar da jini shi ne ginshiƙin tsarin tsarin kiyaye kowacce lafiya amma wannan ya ta'allaƙa ne ga yawan bayar da gudunmawa da kuma ingantattun kayayyakin lafiya .
The latest WHO global status report on road safety 2023 shows that, since 2010, road traffic deaths have fallen by 5% to 1.19 million annually.
Rahoton matsayin hukumar WHO na baya-bayan nan game da aikin tsare hanyoyin mota na shekarar 2023 ya nuna cewa, tun daga shekarar 2010, mace-macen ababen hawa ya ragu da kashi biyar cikin ɗari zuwa miliyan ɗaya da ɗigo goma sha tara a duk shekara.
WHO data show that almost all of the global population (99%) breathe air that exceeds WHO guideline limits and contains high levels of pollutants, with low- and middle-income countries suffering from the highest exposures.
Bayanan WHO sun nuna cewa kusan duk yawan al'ummar duniya (99%) suna shaƙa da fitar da iska wadda ta shige ƙa'idojin da WHO gindaya kuma tana ɗauke da magurɓata da yawa da kuma ƙasashe masu ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga a matsayin waɗanda suka fi gamuwa da wannan barazanar.
“Trans fat has no known health benefit, but huge health risks,” said Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, WHO Director-General.
Trans-fat ba shi da wani sanannen amfani ga lafiya, sai dai babban haɗari ga kiwon lafiya, in ji Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na WHO.
In some cases, this allows a unit of donated blood to meet the needs of more than one patient and is an important aspect of the transfusion train.
A wasu yanayin wannan yana bada dama ga jinin da aka sa da ya yi daidai da buƙatar mara lafiya fiye da ɗaya kuma wannan abu ne mai mahimmanci a ɓangaren gudunmawar bayar da jini.
The purpose of WHO’s Global Strategy on Digital Health is to support countries in strengthening their health systems through the application of digital health technologies and achieve the vision of health for all.
Manufar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO game da shirin Tsarin Duniya (Global Strategy) shi ne samar da tallafi ga ƙasashen duniya don ƙarfafa harkar lafiyarsu ta hanyar yin anfani da fasahohi na harkar lafiya ta yanar gizo kuma a cimma manufa na samun ingantacciyar lafiya ga kowa.
Greenhouse gas emissions that result from the extraction and burning of fossil fuels are major contributors to both climate change and air pollution.
Kona makamashin irin su gawayi ko mai da fitar da sinadaran gas ɗin da suke cutarwa suna taimakawa wajen kawo canjin yanayi da gurɓatar iska.
When will it stop?
Yaushe zai tsaya?
Prevalence: Deafness and hearing loss are widespread and found in every region and country.
Mamaya: Matsalar kurumtaka da rasa ji sun zama ruwan dare kuma ana samun su kusan a ko ina.
Health taxes can be a revenue booster over the short and medium term.
Karɓar harajin harkar lafiya zai iya hana haɓaka kuɗin shiga a ƙanƙanin lokaci da matsakaicin lokaci.
When many people die in natural disasters or armed conflict, the presence of these bodies is distressing for affected communities.
Lokacin da mutane da yawa suka mutu a cikin bala'o'i ko rikici na makamai, ƙasancewar waɗannan gawarwakin yana damun al'ummomin da abin ya shafa.
A vaccine also exists to prevent infections of hepatitis E (HEV), although it is not currently widely available.
Da akwai kuma maganin riga-kafi don kariyar cutar hanta E (HEV), duk da a yanzu bai wadata ba.
A further two, Al-Kheir Hospital and Nasser Medical Complex, are only minimally functional and now inaccessible.
Ƙarin wasu guda biyu, Al-Kheir da Nasser Medical Comlex, su ne kawai suke yin aiki kaɗan kuma yanzu ma ba za a iya isa gare su ba.
Today in Libya, Red Cross and WHO teams are working directly with authorities, communities and the Libyan Red Crescent Society, supporting them with guidance, materials, and training.
A yau a Libya, ƙungiyoyin Red Cross da WHO suna aiki kai tsaye tare da hukumomi, al'ummomi da ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Libya, suna tallafa musu da jagora, kayan aiki, da horo.
Symptoms: Many people with hypertension do not notice symptoms and may be unaware there is a problem.
Alamun cutar: Yawancin mutanen dake da hawan jini basa kula da alamun cutar sannan ba lallai su san cewa da akwai matsala ba.
The disease is most dangerous in infants, and is a significant cause of disease and death in this age group.
Cutar ita ce mafi hatsari ga jarirai, kuma ita ce babbar sanadin kamuwa da cututtuka da mace-macen yara a wancan shekaru.
“COVID showed the world how vulnerable we all are and what needed fixing in the global public health architecture if we are to be better prepared for the next big event and the tone of the discussions during this week’s meeting clearly shows that everyone wants to ensure that this process is successful.”
Annobar Kwabid ta bayyana wa duniya irin raunin da muke da shi bakiɗaya da kuma buƙatar da a duniya ake da ita na inganta kiwon lafiyar al'umma matuƙar dai muna son zama cikin shirin ko-ta-kwanan abin da je ya zo kuma yadda tattaunawar wannan mako ta wakana, ya nuna ƙarara irin yadda kowa ke son ganin an cimma wa wannan buri.
The live-attenuated quadrivalent dengue vaccine developed by Takeda (TAK-003) has demonstrated efficacy against all four serotypes of the virus in baseline seropositive children (4-16 years) in endemic countries and against serotypes 1 and 2 in baseline seronegative children.
Allurar rigakafin zazzaɓi mai sa ciwon jiki wadda ta ƙasance mai rai, da Takeda (TAK-003) ya ƙirƙirao ya nuna tasiri a kan dukkan nau'ukan ƙwayar cutar guda huɗu a cikin yara masu saurin kamuwa da cutar ( 'yan shekaru 4-16) a cikin ƙasashen da ke fama da cutar, kuma a kan nau'uka na 1 da 2 a cikin yara na asali na seronegative.
It includes an increased number of “best buys”, giving countries of every income level more options to save more lives from the world's top killers.
Ya haɗa da ƙarin adadin da aka baiwa dukkan ƙasashe domin samun damar ceton rayuka.
They also integrate early detection and comprehensive treatment of cancer for people living with HIV.
Har ila yau, sun assasa hanyar ganowa da wuri da kuma samar da maganin cutar kansa ga mutanen da ke ɗauke da kwayar cutar HIV.
WHO supports Member States as they implement plans to promote access to quality health services for all.
"Hukumar lafiya ta duniya"(WHO) tana tallafawa ƙungiyoyin ƙasashe yayin da suke aiwatar da tsare-tsare don inganta samun kayayyakin aikace-aikace masu inganci na kiwon lafiya ga kowa.
The Committee recognizes the concerns regarding the lengthy duration of the polio PHEIC and the importance of exploring alternative measures, including instituting a polio IHR Review Committee that could make standing recommendations, and encourages further discussion regarding these alternatives.
Kwamitin ya bayyana damuwa matuƙa game tsawon lokacin da cutar foliyon (PHEIC) ta ɗauka, tare da buƙatar samo sabbin matakan kawo ƙarshen ƙwayar cutar, kamar samar da kwamitin da zai bayar da shawarwari game da ƙwayar cutar. Sannan da yawaita tattauna mas'alar da nufin samar da mafita.
Ash and chemicals from the eruption can also generate risk of food and water contamination, and compromise basic services, like water, transportation, communications and health services.
Ɓurɓushin tokar da wasu kyamikal da ake samu daga aman balkano na iya gurɓata abinci da ruwan sha, da kuma shafar ayyuka na samar da ruwa da sufuri da sadarwa da kuma lafiya.
ensure appropriate food supplementation
Tabbatar da samar da abincin da ya dace.
Whole-of-society engagement is crucial to build integrated approaches.
Shigar da al'umma baki ɗaya nada muhimmanci wajen gina dunƙulallun tsaruka.
These factors are most evident in northern Yemen, northern Nigeria, south central Somalia and eastern DRC, but also in northern Mozambique.T
Waɗannan abubuwan sun fi bayyana a arewacin Yemen, arewacin Najeriya, kudu maso tsakiyar Somaliya da gabashin DRC, da kuma arewacin Mozambique.
States infected with WPV1, cVDPV1 or cVDPV3.States infected with cVDPV2, with or without evidence of local transmission:
Akwai ƙasashen da suka kamu da nau'in cutar shan-inna ta WPV1 , cVDPV1 ko cVDPV3, da ƙasashen da suka kamu da nau'in ƙwayar cutar cVDPVs ba tare da ganin alamun yaɗuwar cutar;:
Hospitalization is recommended only for severe cases of pneumonia.
Ana riqe mai fama da cutar ne a asibiti kawai a lokacin da cutar tayi tsanani.
damaging basic infrastructure, such as food and water supplies and safe shelter.
yana mai lalata ababen more rayuwa kamar su abinci da samar da ruwa da ingantaccen muhalli.
The PRCS staff member was released later that night after joint UN efforts.
An saki ma'aikacin ma'aikacin PRCS daga baya a wannan dare bayan kokarin hadin gwiwa na Majalisar Ɗinkin Duniya.
The final decision on awarding a malaria-free certification rests with the WHO Director-General, based on a recommendation by the independent Technical Advisory Group on Malaria Elimination and Certification.
Matakin ƙarshe kan bayar da takardar shedar ƙasa kaza ba ta cutar zazzaɓin cizon sauro ya rataya ne a hannun babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, bisa shawarar Independent Technical Advisory Group on Malaria Elimination and Certification.
These taxes are considered win-win-win policies because they save lives and prevent disease while advancing health equity and mobilising revenue for the general budget.
Waɗannan harajin, tsari ne da suke da amfani a kowanne ɓangare saboda suna tserar da rayuka da kuma kare faruwar cututtuka a lokaci guda kuma suna bunƙasa daidaiton harkar lafiya da tara kuɗin shiga domin kasafin kuɗin ƙasa gaba ɗaya.
Evidence of this includes the high transmission in DR Congo with spread of cVDPV2 to Burundi and Malawi.
Shaidar hakan ta haɗa da yawaitar yaɗuwar cutar a DR Congo tare da yaɗuwar cVDPV2 har zuwa Burundi da Malawi.
The World Health Assembly urges countries to develop national policies and action plans and to build institutional capacities on occupational health;
Majalisar kula da lafiya ta duniya ta bukaci kasashe da su bunkasa manufofi da tsare-tsare na kasa domin samar da ayyukan ci gaba a fannin aikin kiwon lafiyar.;
Technical updates were received about the situation in the following countries: Afghanistan, Algeria, Burkino Faso, Kenya, Madagascar, Pakistan, United Republic of Tanzania and Zambia.
An samu sabbin bayanai na fasaha game da halin da ake ciki a ƙasashe masu zuwa: Afghanistan, Algeria, Burkino Faso, Kenya, Madagascar, Pakistan, Haɗaɗɗiyar Tarayyar Tanzania da kumaZambia.
The Government of Nigeria spearheaded action to have noma included in the list of NTDs.
Gwamnatin Nijeriya sun ɗauki matakin don a sanya cutar noma a jerin NTDs.
Encourage residents and long-­term visitors to receive a dose of IPV four weeks to 12 months prior to international travel.
Shawartar mazauna ƙasashen da kuma baƙi da su karɓi allurar rigakafi (IPV) ta tsawon makwanni 12 gabannin su yi bulaguro.
Gender inequality hinders progress to fulfill everyone’s right to health.
Rashin daidaiton jinsi na hana kowa cigaba wajen samun 'yacin lafiya.
The antibiotic of choice is amoxicillin dispersible tablets.
Maganin ƙwayoyin cuta na zaɓi shine qwayar amoxicillin.
Environmental or other isolation of WPV1 or cVDPV (no poliovirus case): 12 months after collection of the most recent positive environmental or other sample (such as from a healthy child) PLUS one month to account for the laboratory testing and reporting period.
Bayan samun tabbacin babu ƙwayar cutar shan-inna, sai aka samu rahoton ɓurɓushin cutar a yankin ko kuma aka samu samfurin cutar a tare da wani lafiyayyan yaro, sai a sake jinkirtawa tsawon watannin 12 bayan karɓar samfurin gwajin na ƙarshe. Sannan kuma sai a ƙara wata ɗaya domin gwaje-gwaje a ɗakin gwajin kimiyya kuma a sake gabatar da rahoton. Domin tabbatar da an gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi da nufin tabbatar da ko akwai ƙwayar cutar ta shan-inna.
The Committee’s position has been evolving over the last several months.
Matsayar kwamitin ta fara bayyana a cikin watanni da dama da suka wuce.
Health promoting schools
Makarantun inganta lafiya
The disease is characterized by an abrupt onset of fever, which is frequently accompanied by joint pain.
Alamar cutar na farawa ne da faruwar zazzaɓi kwatsam, wanda ko yaushe yake faruwa tare da ciwon gaɓoɓi.
Optimizing brain health by addressing these determinants not only improves mental and physical health but also creates positive social and economic impacts that contribute to greater well-being and help advance society.
Bunƙasa lafiyar ƙwaƙwalwa ta hanyar magance waɗannan abubuwan ba wai kawai yana bunƙasa ƙwaƙwalwa ba kawai yana ma samar yanayin zamantakewa da tattalin arziƙi wanda suke temakawa walwala .
Three new articles on compliance and implementation were also discussed, as well as new articles related to the public health response, such a proposal for finance mechanisms, access to health products, technologies and know-how during public health response,” said Dr Ashley Bloomfield, former Director-General of Health, New Zealand and Co-Chair of the IHR Working Group.
Tsohon darakta-janar na lafiya a New Zealand kuma ɗaya daga cikin shugabannin Kwamitin Kula da Dokokin Lafiya ta Duniya, Dr Ashley Bloomfield, ya ce, an kuma tattauna kan sabbin ƙudurori uku da suka shafi bin ƙa'ida da aiwatarwa da kuma wani sabon ƙuduri kan kiwon lafiyar al'umma kamar ba da shawara game da hanyar samar da kuɗi, damar samu kayayyakin lafiya, fasahohi da horaswa a yayin aikin kiyaye lafiyar al'umma.
For protection during outbreaks of chikungunya, clothing which minimizes skin exposure to day-biting mosquitoes is advised.
Domin kariya lokacin ɓarkewar cutar Cikanganya, ana ba da shawarar sa kayan da za su rage bayyanar fatar mutum ga saurayen da suke cizo da rana tsaka.
Provide to the Director-General a regular report on the implementation of the Temporary Recommendations on international travel.
Bawa Babban Darakta Janar rahoto akai-akai kan aiwatar da Shawarwari na wucin gadi kan balaguro daga wata ƙasa zuwa wata.
Work continues to strengthen preparedness and response for health emergencies
Aiki yana ci gaba da ƙarfafa shirye-shirye da kuma mayar da hankali kan lamurran rashin lafiya na gaggawa
WHO releases the largest global collection of health inequality data
Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar da dogon rahoto kan rashin daidaito na a ɓangaren kiwon lafiya na duniya.
The call was made by WHO Director-General Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus following discussions today with an Israeli non-governmental organization, the Hostages and Missing Families Forum, that represents families of the abducted people.
Kiran ya fito ne daga bakin Darakta janar na WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus biyo bayan tattaunawar da su ka yi a yau tare da kungiya mai zaman kanta a Isra'ila, da waɗanda aka kama, da kuma kungiyar ɓacewar iyalai wato Missing Family Forum a turance, wanda ya wakilci Iyalan da aka yi garkuwa da su.
In severe cases though, surgery may be necessary.
A cutar mai tsanani kuma, za a iya buƙatar yin tiyata.
This convergence may give rise to migration from games to gambling and co- occurrence of the two disorders.
Wannan haɗuwar kan iya jawo ƙaura daga wasanni zuwa caca da kuma afkuwar cututtukan guda biyu.
WHO has guidance that covers all WHO Regions to help reduce the prevalence of anaemia through prevention and treatment.
WHO tana da ƙa'idar da ta game duk wasu yankin WHO domin temakawa wajen rage yaɗuwar anemiya ta hanyar riga-kafi da bada magani .
The research released in Environment International finds that outdoor workers carry a large and increasing burden of non-melanoma skin cancer and calls for action to prevent this serious workplace hazard and the loss of workers’ lives it causes.
Binciken da aka fitar a Environment International ya gano cewa ma'aikata a waje suna ɗaukar nauyi mai yawa da yawa na kansar fata wanda ba melanoma ba ta haifar kuma ya yi kira da a dauki mataki don hana wannan mummunan hatsarin wurin aiki da asarar rayukan ma'aikata da yake haifarwa.
Many thousands more, also with wounds or other health needs, cannot access any kind of care.
Wasu dubunnan kuma, waɗanda kuma ke ɗauke da ciwuka ko wasu matsalolin da ke buƙatar kula da lafiya, ba za su iya samun kowace irin kulawa ba.